28 Maris 2026 - 13:38
Source: ABNA24
Iran: Sojojin Amurka Sama Da 500 Ne Suka Sheka Lahira

Biyo bayan hare-haren Iran kan wuraren Amurka an samu rasuwa mai yawa ga sojojin Amurka sama da 500 a Dubai

بسم الله قاصم الجبارین

Da sunan Allah Mai Karya Jabberai:

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Hedkwatar Khatamul-Anbiya; A baya mun yi gargadin cewa sojojin Amurka sun gudu sun boye a wajen sansanoninsu saboda hare-haren masu ƙarfi na dakarun tsaron mu da kuma ruguza sansanoninsu a yankin. A cikin 'yan sa'o'i da suka gabata, an gano maboyarsu guda biyu, a wurin buya na farko na ɗauke da mutane sama da 400, kuma a maboyar ta biyu, sama da mutane 100 ne ke boye a Dubai, wadanda dukkansu an gano su, kuma an kai musu hari da makamai masu linzami da jirage marasa matuka na dakarun juyin juya halin musulunci bangaren sojojin Sama. Kuma an tabbatar da samin rasa rayuka da raunuka masu yawa. Motocin daukar marasa lafiya a tsawon sa'o'i suna jigilar mutanen da suka mutu da raunata daga kwamandojin Amurka da sojoji. 

Dole ne Trump da kwamandojin sojojin Amurka su fahimta da kyau cewa yankin zai zama makabarta na sojojin Amurka kuma ba za su sami wani zabi illa mika wuya ga nufin Allah na jaruman Al'umma da jaruman Musulunci ba. 

و ما النصر الا من عندالله العزیز الحکیم

Kuma nasara tana ga Allah shi kaɗai mabuwayi mai hikima

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha